Accessibility links

An dangata rashin karkon wasu daga cikin kayayyakin da ake shigowa dasu Najeriya daga kasar China

An dangata rashin karkon wasu daga cikin kayayyakin da ake shigowa dasu Najeriya daga kasar China, akan algus din wasu ‘yan kasuwa masu bukatar a sarrafamasu kayayyaki marasa inganci domin cin kazamar riba.

Wani dan kugiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta jihar Kano Alhaji Uba Tanko Mijinyawa, ne ya furta haka a wata hira da suka yi ta wayar tarho daga China da wakilin mu Aliyu Mustapha.

Yace sunje China, ne a bisa gayyatar ma’aikatar bunkasa ciniki da masana’antu na kasar China, domin gani da ido yanda abubuwa ke gudana da kuma yanda zata bunkasa hurda da kasashen Afirka.

Kimanin kasashen Afirka , goma sha takwas kasar ta China, ta gayyata inda suka ziyarci masana’antu da dama kamar nayin Motoci da janareto da nayin katafiloli.

XS
SM
MD
LG