Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Girke Makamai Masu Linzame


Woody Island.

Ma’aikatar tsaron Taiwan tace China ta girka daya daga cikin irin waanan makaman ne akan tsibirin Woody Island

China ta girke wasu makamai masu linzame akan daya daga cikin tsibirran da ake rigima da ita a kansu dake cikin babbar tekun kudancinta, matakin da akace ya tada hankalin makwabtanta.

Ma’aikatar tsaron Taiwan tace China ta girka daya daga cikin irin waanan makaman ne akan tsibirin Woody Island, wanda bangare ne na rukunin tsibirran Paracel.

Wasu hotunan da tashar telebijin ta Fox ta nuna, sun gwada wasu jerin makamai biyu masu hancin bindigogi takwas-takwas tareda wata babbar na’urar tantance motsin abubuwan dake cikin sararin samaniya.

Sai dai kuma Ministan harakokin wajen China, Wang Yi yace wadanan rahotonnin kire-kiren kafofin watsa labaran kasashen Yammacin Turai ne kawai, ba gaskiya bane.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG