Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Kotu Ta Bada Belinsa Akan Dala Miliyan 50


Iran ta sha fama da jerin takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta kakaba ma ta tun daga 1979

Lauyoyin wani dan Turkiyya dan asalin kasar Iran, wanda aka kama a watan Maris kan zargin hada baki a saba ma takunkumin da Amurka ta kakaba ma Iran, sun bukaci kotu ta ba da belinsa kan dala miliyan 50 kafin a fara shari'arsa.

Reza Zarab na daya daga cikin mutane 3 da ake zargi kan abin da masu gabatar da kara su ka ce wata muna-muna ce ta tsawon shekaru 5 ta miliyoyin daloli da aka yi a madadin gwamnatin Iran da wasu kamfanoni.

Iran ta sha fama da jerin takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta kakaba ma ta tun daga 1979, da su ka hada da hana duk wata huldar kasuwanci tsakanin kamfanonin Amurka da duk wani kamfani mai alaka da Iran ko gwamnatinta. Wadancan sun banbanta da takunkuman da su ka biyo baya, wadanda aka kakaba ma ta saboda shirinta na nukiliya, wadanda aka dage ma ta a farkon wannan shekarar.

A watan Maris an tuhumi Zarrab da mukarrabansa da amfani da wasu kamfanoni a Iran, da Turkiyya da wasu kasashe a duniya, wajen gudanar da harkar cinakayya ta yadda bankunan Amurka ba za su san cewa ana harkokin ne a madadin kamfanonin Iran ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG