Kamfanin kera motocin Toyota ya bada sanarwar a maido da motoci fiye da miliyan uku a duk fadin duniya a saboda matsalar da aka gano a jikin jakar iska da kare mutum a sakamaon hatsari da ake cewa air bag da turanci.
Motoci samfurin Prius hybrid da “Prius plug in” da kuma samfurin Lexus CT200 da aka kera tsakanin watan Oktoban shekara ta dubu biyu da takwas da watan Afrilun shekara ta dubu biyu da goma sha biyu suna daga cikin motoci da aka bukaci a maida kamfanonin da aka sayo su.
Haka kuma samfurin Corolla mai farin jinin da aka kera tsakanin shekara ta dubu biyu da shidda da dubu biyu da goma sha biyar suma an bukaci a maida su domin an gano matsala a cikin idan ake adana mai, da ake zaton, kila ko ba jima ko ba dade ya tsage ya hadasa yoyon mai.
Wannan sanarwar, shine matsala na baya bayan nan daga cikin matsalolin da kamfanin yin motoci Toyota ya ke fuskanta.