Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Dar-Dar A Wasu Biranen Amurka


Yayinda ake juyayin wannan abinda ya faru a Louisiana hakan ta sake faruwa a jihar Minnesota

Ana zaman dar-dar a wasu birane na Amurka a sanadin harbin izgilanci da ‘yansanda suka yi wasu wa wasu fararen hula, Bakaken Fata, wanda wasu ke ganin kamar akwai ganganci a cikinsu.

Na farko ya faru ne jiya a birnin Baton Rouge na jihar Louisiana inda jiya da dare dimbin mutane suka fito, kowa dauke da fitillun kyandir, suka tsaya a gaban wani dan shago inda a nan ne ‘yan sanda suka bindige wani Bakar Fata.

Wasu sun dauki kisan a kan wayoyinsu na hannu, abinda kuma aka warwatsa ko ina, abinda ya dada fusata mutane wadanda daman sun gaji da ganin yadda ake ta kara samun abkuwar irin wannan al’amarin na ‘yansanda masu kashe mutane ta hanyar harbe su.

Wanda aka kashe a gaban wannan shagon a can Louisiana wani Bakar Fata ne mai suna Alton Sterling, 37, wanda akace ya tsaya gaban shagon ne, yana sayarda faya-fayinsa na CDs a lokacinda abin ya faru.

Yayinda ake juyayin wannan abinda ya faru a Louisiana ne sai gashi kuma irin hakan ta sake faruwa a jihar Minnesota inda wani dansanda ya bindige wani Direba mai suna Philando Castile, 32, har lahira bayanda dansandan ya tsaida motar mutumen a garin Falcon Heights.

Wanda aka kashe yana tareda wata mace da yaro jinjiri a cikin motar lokacinda dansandar ya bindige shi.

XS
SM
MD
LG