Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Phillippine Yayi Kokari Akan Safarar Muggan Kwayoyi


Shugaban Kasar yasa a jami’ar De La Salle dake Philippines. Rodrigo Duterte
Shugaban Kasar yasa a jami’ar De La Salle dake Philippines. Rodrigo Duterte

A Philippines an sami raguwar aikata manyan laifuka fiye da kashi 1 cikin biyar, a shekarar nan, abinda ya dadadawa jama’ar kasar rai yake kuma nuna cewa ta yiwu yaki da masu safara da shan miyagun kwayoyi da shugaba Rodrigo Duterte ya kaddamar, wanda ya janyo cece-ku-ce daga kasashen duniya game da batutuwan hakkokin jama’a, na dakile aikata manyan laifuka.

Sabawa jama’a da dukiyoyinsu ba bisa ka’ida ba ya ragu da kashi 21.8 daga watan Janairu zuwa watan Nuwamban da ya gabata a shekarar nan, idan aka kwatanta da wannan lokacin shekarar 2016, a cewar wasu alkaluma daga rundunar ‘yan sandan Philippines da kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.

Alkaluman sun nuna irin cigaban da shirin yaki da sha da saffarar miyagun kwayoyi mai cike da takaddama da Duterte ya kaddamar ke samu, da kuma kokarin da ‘yan sandan kasar suka yi, a cewar Antonio Contreras, masanin kimiyar siyasa a jami'ar De La Salle dake Philippines.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG