Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DA DANGARI: Tarihin Garin Gadanya A Jihar Kano, Afrilu 30, 2022


Bandiagara, Mali
Bandiagara, Mali

Adamu Ibrahim Dabo Dawakin Tofa na gidan rediyon jihar Kano, ya leka garin Gadanya da ke karamar hukumar Bagwai a arewacin birnin Kano don lalubo tarihinsa.

Washington, DC - Malam Lati Umar Gadanya, wani dattijo kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, ya ce shekaru kimanin dubu daya kenan da kafuwar garin Gadanya. Sunan garin dai ya samo asali ne daga wani da ake kira Gadanyu wanda ya fito daga garin Moji a karamar hukumar Bagwai, a cewarsa.

Malam Umar ya kuma ce ana yiwa garin kirari da “Gadangan ta Kawaji, Gadon Kaya hana barci, tuwon kaya miyar allura, yaro ina da mai hadiya. Ma’ana, duk mutanen Gadanya jarumai ne ta kowanne bangare.

Ya kuma ce a lokacin yaki shekaru da dama da suka wuce, babu mai iya cin garin Gadanya da yaki saboda kaya ta kan kewaye shi, ko kuma duk wani da zai shigo garin da mugun nufi to ba zai yi nasara ba saboda garin yakan bace sai dai a ga kaya.

Hausawa da Fulani su ne dai manyan kabilun da suka kafa garin Gadanya sai kuma wasu daidaiku kamar Barebari da suka zo daga baya.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

Da Dangari: Tarihin Garin Gadanya a Jihar Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:08:27 0:00

XS
SM
MD
LG