Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwar Katakon Birnin Accra, Ghana


Yayin da ake hadahadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano
Yayin da ake hadahadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin Kasuwa na wannan makon ya kai ziyara babbar kasuwar Timber Market da ke birnin Accra a kasar Ghana.

Washington, DC - Wakilin muryar Amurka Ridwan Abbas ya tattauna da wasu masu hada hadar cinikayya a kasuwar ta Timber Market.

Jibrin Abdullahi, dan kasuwa ne wanda ya bayyana cewa ya gaji sana’ar saida itace daga kakanninsa ne da suka kafa kasuwar.

Ita dai kasuwar ta na da sassa dabam daban da suka ha da fannin sarrafa katako, saida karahuna, saida hatsi, da sauransu.

Ana kawo itacen ne daga dazuzzuka da yawa na Ghana, a cewar Jibrin.

Yakuba Alpha, wani dan kasuwa mai shekara tamanin da daya, ya ce a shekarar 1962 suka fara cinikayyar itace a kasuwar.

Hukumomin kasar Ghana dai na ci gaba da daukar matakan raya itatuwa, amma masu sana’ar katako sukan bude kamfani ta yadda zasu samu izinin sarar itatuwa ta hanyar da ta dace.

XS
SM
MD
LG