Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISWAP Ce Ta Kai Harin Ondo – Gwamnatin Najeriya


Taron kwamitin tsaro a Najeriya (Hoto: Facebook/Fadar shugaban Najeriya)

Ministan ya kuma jaddada cewa, harin na Owo, ba shi da wata nasaba da kabilanci ko addini.

Rahotanni daga Najeriya, na nuni da cewa, hukumomin kasar sun dora alhakin harin da aka kai akan cocin St Francis da ke garin a Owo a jihar Ondo akan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP.

A karshen makon da ya gabata, ‘yan bindiga suka bude wuta a mujami’ar wacce ke kudu maso yammacin Najeriya, yayin da masu ibada ke shirin kammala taron addu’o’insu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ya fadawa manema labarai hakan bayan taron kwamitin tsaron kasa da ya gudana a ranar Alhamis a Abuja, babban birnin Najeriya kamar yadda jaridar Daily Trust da gidan Talbijin na Channels suka ruwaito.

Taron kwamitin tsaron Najeriya (Hoto: Facebook/Fadar shugaban Najeriya)
Taron kwamitin tsaron Najeriya (Hoto: Facebook/Fadar shugaban Najeriya)

A cewar Aregbesola, bincike ya nuna cewa kungiyar ta kai harin ne da zimmar gwara kan ‘yan Najeriya don su kaure da fadan kabilanci da addini.

Ya kara da cewa, tuni an ba jami’an tsaron umarnin su farauto ‘ya’yan kungiyar da su fuskanci tuhuma

Ministan ya kuma jaddada cewa, harin na Owo, ba shi da wata nasaba da kabilanci ko addini, yana mai cewa aika-aikar da kungiyar ta ISWAP take yi, shi ma ba shi da nasaba da addini.

Harin wanda har ila yau jikkata wasu masu ibada da dama.

Dubi ra’ayoyi

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG