Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Amurka Kamfanoni Na Ta Kaurace Ma Kungiyar Ma'abuta Bindigogi


Wani matashi na auna bindiga a wani babban taron NRA
Wani matashi na auna bindiga a wani babban taron NRA

A cigaba da nuna kyama ga kungiyar ma'abuta bindigo ta NRA mai son wanzar da makamai a Amurka, kamfanoni na ta yanke huldar kasuwanci da kungiyar, bayan kashe mutane da dama da wani matashi ya yi da bindiga kwanan nan.

An samu karin kamfanoni 3 da su ka yanke huldar kasuwanci da kungiyar ma’abuta bindigogi ta NRA, yayin da kungiyoyin rajin takile yaduwar bindigogi su ka zafafa matsin lamba kan kamfanoni, don su kawo karshen duk wata hulda da takwarorinsu masu harkar bindigogi ko kera su, bayan harbe-harben da aka yi a wata makaranta a Florida a makon jiya.

‘Yan gwagwarmaya sun gabatar da koke-koke ta kafar ‘yanar intanet,’ inda su ka bayyana sunayen kamfanonin da ke bayar da rangwame ga ‘yan kungiyar ma’abuta bindigogi ta NRA, a wani mataki na takura irin wadannan kamfanonin su nisanta kansu daga kungiyar rajin jaddada ‘yancin mallakar bindiga.

Kamfanonin da su ka kawo karshen yarjajjeniyar yin rangwame ga ‘yan kungiyar NRA daga jiya Jumma’a sun hada da kamfanin inshore na MetLife, da kamfanin hayar mota na Hertz, da kuma kamfanin Symantec, mai softuwayar yaki da manhajar kutse

Wannan ya biyo bayan daukar irin wannan matakin da wasu kamfanonin su ka yi tun a farkon wannan satin, wadanda su ka hada da bankin First National of Omaha, da otal din Wyndham da kamfanin hayar motoci na Enterprise da kuma kamfanin rukunin otal-otal na Best Western.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG