A wannan shirin mun bada labarin wani Danfulani wanda shanunsa suka bace, da kuma Danborno manomi da dukansu suka nemi su cuci juna.
Sausari shirin ka ji abinda ya faru, ka kuma gaya mana ko wanene a cikinsu ya fi mugunta.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.