Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Labarin Mai Shan Giya Da Sunan Abokai, Nuwamba 05, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A wannan shirin mun bada labarin wani mutum wanda ya ke shan kwalbar giya uku duk lokacin da ya shiga gidan giya. Da mai shagon ta kula da haka sai wata rana ta tambaye shi dalilin da yasa yake shan kwalba uku kullum ba ragi ba kari, sai ya ce wai yana da abokai ne biyu daya a kasar Indiya, dayan kuma a kasar Rasha. Kafin su tafi suka dauki alkawarin za su rika zumunci ta shan giya. Duk wanda zai sha giya sai ya sha wa ’yan uwansa. Dalili ke nan da ya ke shan kwalba uku duk lokacin da ya je gidan giya. Sai wata rana mai shagon ta lura ya sha biyu kawai, sai ta tambaye shi wanene cikin abokan ya mutu, sai ya gaya mata cewa, ba wanda ya mutu sai dai shi ne Allah ya shirye shi ya daina shan giya, biyun da ya sha, ya sha wa abokan nasa ne da ke India da kuma Rasha.

Saurari cikakken shirin:

A Bari Ya Huce: Labarin Mai Shan Giya Da Sunan Abokai-24: 00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:24:31 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG