Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Labarin Malami Da Dalibi Mai Yawan Wasa A Aji, Oktoba 30, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A wannan shirin mun bada labarin wani malamin makaranta da ya ba dalibansa labarin aikin soja daga shigar su, zuwa horon da su ke samu, da kuma aikinsu a bakin daga. Bayan ya basu labarin sai ya ce su dauka su ne aka dauka soja aka tura bakin daga, yana so su rubuta abubuwan da su ka faru lokacin da su ke filin daga. Bayan dan lokaci malamin ya zaga ya tattara takardun domin ya ga amsoshin da daliban su ka rubuta sai ya tarar wani yaro mai yawan kin ji bai rubuta komi ba. Malamin ya tambaye shi dalilin da ya sa bai rubuta ko mi bai, sai yaron ya cewa malamin, ai ni Mallam "tun a farkon yakin aka kashe ni."

Saurari cikakken shirin:

A Bari Ya Huce: Labarin Malami Da Dalibi Mai Yawan Wasa A Aji-24: 00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:25:01 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG