Boni Yayi ya bar ofis bayan kamala wa’adin mulkinsa biyu, tare da jadada kasancewar Benin abin koyi a fannin damokaradiya a nahiyar dake fama da fadi tashin siyasa inda shugabanni suke yiwa kundin tsarin mulkin kasashensu gyaran fuska domin su ci gaba da zama kan karagar mulki.
Ya shaidawa manema labarai lokacin da ya kada kuri’arsa cewa, yabar kadar tsitsiya madaurinki daya.
Idan babu dan takrar da ya sami rinjaye a zagayen farko, za a gudanar da zagaye na biyu cikin makonni biyu.