Accessibility links

Akalla Mata 2,000 Ne Shirin Tallafawa Mata Na Jihar Gombe Ya Yaye

  • Aliyu Imam

'Yan mata masu tallace tallace a Najeriya.

Shirin tallafawa mata su dogara da kansu ya yaye kamar mata 2,000, kuma aka basu jarin Naira dubu hamsin.

A kokarin yaki da talauci da rashin ayyukan yi da yafi addabar mata a Najeriya musamman a jihohin da suke yankin arewa maso gabas, matan gwamnoni da suke shiyyar sun zabura wajen yaki da wannan yanayi.

Uwargidan gwamnan jihar Gombe karkashin shirin 'yanto mata daga akubar talauci d a jahilci ta yaye akallla mata dubu biyu da aka koyawa sana'o'i daban daban, sannan kuma aka basu jari da bai kasa Naira dubu hamsin ko wani mutum ba.
Kamar yadda zaku ji cikin wannan rahoto da Sa'adatu Mohammed Fawu ta aiko mana.

XS
SM
MD
LG