Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Hadin Kan Addinai a Abuja


Wasu matasa a taron hadin kan Musulmai da Krista da ya gudana a Abuja
Wasu matasa a taron hadin kan Musulmai da Krista da ya gudana a Abuja

Manufar taron hadin kan addinai a Abuja shi ne shimfida karfafa hanyar neman zaman lafiya tsakanin mabiya addinan Islama da na Krista.

An cigaba da taron matasan addinan Islama da na Krista a Abuja da manufar shimfida hanyoyin karfafa zaman lafiya da cudanya tsakanin addinan Islama da na Krista, da kuma kulla dankon zumunci mai dorewa.

Shugabannin addinan biyu sun jaddada mahimmanci zaman tare da rugumar juna da kaunar juna ba tare da kyamar juna ba. A cewar shugabannin addinan biyu fahimtar juna da kaunar juna su ne matakan farko na tabbatar da zaman lafiya. Hadin kansu shi ne jigo wajen tabbatar da cigaban kasa gaba daya.Suka ce gayyato matasan addinan biyu shi ne matakin farko na binne abubuwan da suka faru a can baya a nan arewa.

Fada John daga bangaren Krista yace yau suna taron nishadi da yin murna domin su nuna wa duniya cewa Musulmai da Krista ka iya zama tare , su yi cudanya tare ba tare da wani tashin hankali ba. Shi kuiwa shugaban matasan Musulmai Abdulrazak Aliyu Mohammed ya kara jaddada dalilinsu na shirya taron. Ya ce suna dada nunawa cewa zaman lafiya tsakanin Musulmai da Krista shi ne zai tabbatar da cigaban kasar. Idan babu zaman lafiya ba za'a yi kasuwanci ba, ba za'a yi karatu ba, ba za'a yi sana'o'i ba, harta ma yin addinin zai gagara. Sabo da waddannan dalilan ya ce suka ga ya kamata su zo su fadakar da juna dangane da mahimmancin zaman lafiya.

Mahalarta taron sun fito ne gada jihohin dake makwaptaka da birnin tarayya Abuja. Wani Fada daga jihar Kaduna amma yana aikin fada a jihar Neja ya ce ya ko yi darusa da yawa a wurin taron. Ya ce ya lura cewa su 'yan uwan juna ne da ka iya zama tare. Ya ce idan matasa suka samu koyaswa mai tasiri da tarbiya mai kyau zasu gane cewa abubuwan da suke gani sun raba su ba gaskiya ba ne.Ita kuma Aisha daga Karu cewa ta yi kamata ya yi su hada kai domin duk su daya suke.

Madina Dauda nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG