Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Abu Zubaydah Ya Bayyyana Gaban Jama'a


Jiya Talata aka ga wani da ake zargin shugaban kungiyar al-Qaida ne da ake tsare dashi a Guantanamo Bay karon farko a bainin jama’a tun shekara ta dubu biyu da biyu.

Abu Zubaydah da aka kama, ba da dadewa ba, bayan harin sha daya ga Satumba shekara ta dubu biyu da daya, yana neman a sake shi.

Zubaydah, dan shekaru arba’in da biyar yanzu, da lauyoyinsa, suna cewa, bashi da hatsari ga Amurka.An bada labari cewa, yace yana so ya koma wurin danginsa ya fara sana’a bayan ya sami damar shiga al’umma.

Amurka tana zargin Zubaydah Bapalasdine da kasancewa daya daga cikin manyan kungiyar al-Qaida lokacin da aka kama shi a Pakistan a shekara ta dubu biyu da biyu, sai dai tun lokacin ta janye wannan zargin.

Zubaydah ya bace a cikin rububi a jerin wadanda ma’aikatar leken asirin Amurka ta tsare kafin aka tsareshi a hukamance a Guantanamo cikin watan Satumba shekara ta dubu biyu da shida. Kuma ya shafe sama da shekaru goma ba tare da an tuhumeshi da aikata wani laifi ba.

Rahotannin ma’aikatar leken asirin da aka fitar a watan Yuni sun nuna Zubaydah ya fuskanci tsauraran matakan bincike da suka hada da nutsar da shi a ruwa sau tamanin da uku, ko da yake masu binciken sun bayyana cewa, sun hakikanta cewa, bashi da wani sauran bayanin da zai yi masu.

Wani bayani a rahoton ya bayyana cewa, idan ya mutu, a kona gawarsa, kuma sabili da irin hanyar tatsar bayanan da za a yi amfani da ita, ya kamata a killace shi, ya zauna shi kadai iya tsawon rayuwarsa.

Daya daga cikin bayanan da aka kara a rahotanni a baya- bayan nan na cewa, hadin kan da Zubaydah ya bayar bashi da wata alaka sosai da hanyoyin tatsar bayanan da aka yi amfani da su.

Bisa ga nayanin da aka karanta a wajen sauraron bahasin jiya talata da wani jami’in sojan Amurka da yake wakiltarsa ya karanta, Zubaydah yace bashi da niyyar cutar Amurka ko wata kasa, ya kuma sha bayyana cewa, kungiyar IS ta wuce gona da iri.

XS
SM
MD
LG