Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kwango Jam'iyyun Hamayya Zasu Gana da Jakadan Amurka da Na Tarayyar Turai


Shugaban Congo, Denis Sassou-Nguesso mai neman ta zarce

A Kwango shugaban 'yan hamayyar kasar yace 'su da kungiyoyin fararen hula zasu gana da jakadun Amurka dana Kungiyar Tarayyar Turai yau Alhamis, domin su tattauna kan yanayin siyasar kasar.

Shugaban jam'iyyar hamayyar ta MCDDI da ake kira Perfect Kolelas, yace babban abun da zasu tattauna shi ne neman hanyoyin kawo karshen tarzomar da take ci ahalin yanzu a kasar. Kolelas yayi kira ga hukumomin kasa da kasa ciki harda Kungiyar Tarayyar Turai da su sa baki domin su tabbatar da cewa ba'a yiwa tsarin mulkin hawan-kawara ba.

Kalaman Kolelas sun zo ne bayan da 'Yansanda suka kara da magoya bayan 'yan hamayya har aka kashe akalla mutum hudu wasu da dama kuma suka jikkata. Matasa dake goyon bayan 'yan hamayyar suna zanga zangar nuna adawa ne da shirin kuri'ar raba gardama da aka ayyana rana r Lahadi mai zuwa domin cire kayyade shekarun dan takarar shugaban kasa kada ya wuce 70 da doka ta tanada yanzu, da kuma kayyade wa'adi.

Kolelas yace sun yi magana da jakadan Amurka da na Tarayyar Turai wadanda suka basu shawarar su nemi ganawa da shugaban kasa Denis Sassou Nguesso dan shekaru 72 da haifuwa domin ganin ko za'a bude wata kafar kulla wata sabuwar yarjejeniya.

Perfect Kolelas yace 'yan hamayya da kungiyoyin fararen hula ba zasu yi kasa a gwuiwa ba wajen tabbatar da cewa baa yiwa tsarin mulkin karan tsaye ba.

Amma kafofin yada labaran kasar sun ambaci babban sakataren jam'iyyar dake mulkin kasar LP Pierre Ngolo yace yiwa tsarin mulkin asar kwaskwarima ya zama tilas.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG