Accessibility links

Gobe Litinin Za a Ci Gaba Da Yajin Aiki A Najeriya.

  • Aliyu Imam

Masu zanga zangar kanjanye tallafin mai a wuni na biyar.

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sunce za a ci gaba da yajin aiki gobe litinin sabo da an kasa cimma matsaya kan batun janye tallafin mai.

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sunce za a ci gaba da yajin aiki gobe litinin idan har ba a cimma dai-daito kan tsaida farashin mai a shawarwari da suke yi da gwamnati ba.

Wakilan babbar kungiyar kwadago da ta masu sana’o’in hanu sun bada sanarwa yau lahadi cewa sun janye barazanar tsaida ayukan hakar mai.

A zaman farko da suka yi jiya Asabar, shugabannin kungiyoyin kwadago sunyi shawarwari da shugaba Goodluck Jonathan d a wasu jami’an gwamnati kan janye tallafin mai d a ya fara aiki daga daya ga watan nan. Bayan muhawara na sa’o’I duka sassan biyu suka bayyana cewa ba a cimma dai-daito ba.

Kungiyoyin kwadagon suna son gwamnati ta maida tsohon farashin mai kamin ta janye tallafin dala milyan dubu takwas da take bayarwa.

Shugabannin kungiyoyin sun tsaida yajin aiki na wani dan gajeren lokaci gabannin ganawarsu da shugaba Goodluck Jonathan.

Ahalin da ake ciki kuma shugabannin majalisar dokokin kasa suna gargadi ga jama’a su nisanci kalamai da zasu kara tada hankali da farraka kan kasa.

Madina ta kuma aiko da rahoton cewa gobara ta cinye wani bangare na ofishin akawun majalisar dokokin tarayya Alhaji Salisu Maikasuwa a wunin jiya Asabar.

A ci gaba da rangadin jihohi dake arewa maso gabashin Najeriya inda ake yawan kai hare haren ta’addanci, mataimakin speto janar na ‘Yan sandan Najeriya Audu Abubakar, ya isa jihar Adamawa domin rangadin ganema kansa wurere da tashe tashen hankula suka shafa cikin jihar.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG