Accessibility links

Kungiyar Kwadago Da Gwamnati Sun Tashi Baran Baran

  • Halima Djimrao-Kane

Babu ranar kawo karshen yajin aikin ma'aikata da zanga-zangar da jama'a ke yi akan cire tallafin mai, kamar yadda na cikin hoton nan ke dauke da kwalin da ke cewa "Gaba-Gaba dai gwagwarmaya, ba gudu, ba ja da baya"

Gwamnatin Najeriya da shugabannin kungiyar kwadago sun kasa cimma jituwa

Gwamnatin kasar Najeriya da shugabannin kungiyar kwadagon kasar sun kasa cimma jituwa a tattaunawar da suka yi a jiya Asabar da nufin neman kawo karshen yajin aikin da aka yi mako daya ana yi , amma kungiyar ta janye barazanar ta, ta dakatar da aikin hakar mai.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya, NLC, Abdulwahed Omar ya shaidawa manema labarai cewa ba za a dakatar da ayyukan hakar mai ba, sannan ya fada cewa, “Mu na daukan wadannan abubuwa ne bi da bi” a lafazin shi.

A ganawar farko daga cikin biyun da suka yi a jiya Asabar shugabannin kungiyar kwadagon Najeriya sun tattauna da shugaba Goodluck Jonathan da kuma wasu jami’an gwamnatin akan cire tallafin man fetur, wanda ya fara aiki tun ranar daya daga watan nan na janairu. Amma bayan cukumurdar da bangarorin biyu su ka fuskanta bayan wasu ‘yan sa’o’i da fara tattaunawar, sai su ka tashi baran-baran, ba tare da cimma wata jituwa ba.

Shugabannin kungiyar sun dakatar da yajin aikin na dan wani takadirin lokaci a gabannin tattaunawar su da shugaba Jonathan a jiya Asabar a birnin Abuja, amma sun ce za a ci gaba da yajin aikin a gobe Litinin idan ba a maida tallafin man da aka cire ba.

Shawarar kawo karshen tallafin man da gwamnatin kasar ta yanke, ta sa farashin mai ya rubanya na da sau biyu, kuma ta haifar hauhawar farashin kayan abinci da sufuri. Tun daga wannan lokaci dubban daruruwan ‘yan kasar su ka fara zanga-zangar bayyana fushin su. Su kuma kungiyoyin kwadagon kasar su ka shiga yajin aikin da aka yi kwanaki biyar ana yi wanda kusan baki daya ya gurgunta hada-hada a kasar Najeriya wadda ita ce mafi arzikin mai a nahiyar Afirka.

Daya daga cikin manyan kungiyoyin kwadagon kasar ta ce za ta dakatar da aikin hakar mai idan gwamnatin kasar ba ta maida tallafin mai ba, takun da watakila zai iya shafar tattalin arzikin kasar har ma ya taba farashin mai a duniya.

A halin da ake ciki yanzu, dimbin ‘yan kasar ta Najeriya sun a gaggauta zuwa kantuna da kasuwanni su na cikon kayan abinci, amma kuma da yawan su na fama da tsananin tsadar farashin abincin da ya rubanya na da sau ukku a wasu wurare.

XS
SM
MD
LG