Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Saudiyya Ana Yiwa Rayuwar Mace Mai Fafutikar Neman 'Yancin Mata Barazana


 Manal al-Sharif mace dake fafutikar samarwa mata 'yanci a Saudiyya wadda tace tana samun sakon yiwa rayuwarta barazana
Manal al-Sharif mace dake fafutikar samarwa mata 'yanci a Saudiyya wadda tace tana samun sakon yiwa rayuwarta barazana

A Saudiyya Manal al-Sharif mai fafutikar neman wa matan Saudiyya 'yanci a duk fannin rayuwa ta ce tana samun sakonnin dake yiwa rayuwarta barazana yayinda kasar ke kusa da dage dokar hana mata tukin mota

Mai fafutukar ‘yancin dan adam din nan da ta taimaka wajen fara yakin a bar mata su tuka mota a Saudiyya, ta ce, tana samun sakonnin da ke barazana ga rayuwarta, yayin da aka tunkarin lokacin dage dokar.

A shekarar 2011, an taba rufe Manal al-Sharif, bayan da ta saka wani hoton bidiyonta tana tuki a kasar ta Saudiyya, kasar da ita ce kadai ta haramtawa mata tuki a Duniya.

Al-sharif, wacce yanzu haka take zaune a kasar Australia, ta fadawa kafafen yada labaran cikin gida a jiya Litinin cewa, tana da shirin komawa kasarta, ta kuma tuka mota ta zagaya kasar, idan an dage dokar a ranar 24 ga watan Yuni.

Amma kuma ta yanke shawarar cewa za ta zauna a Sydney,babban birnin Australia, bayan da aka tsare wasu fitattun masu fafutukar ‘yancin dan adam su bakwai a karshen makon da ya gabata a Saudiyyan.

A cewar Al-Sharif, an kira dumbin masu fafutuka a wayar talho, inda aka gargadesu da kada su yi tsokaci kan dokar da ta yi magana kan dage tsari haramta tukin mota ga mata a kasar ta Saudiyya, tana mai cewa mutane bakwan da aka tsare, suna cikin wadanda ke ci gaba da magana kan lamarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG