Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Somaliya An Kashe Wani Shugaban Kungiyar Al-Shabab


Sabbin mayakan kungiyar al-Shabab.

Gwamnatin Somaliya ta ce an kashe Shugaban kungiyar al-Shabab na yankin Shabelle ta kasa da wasu mukarrabansa uku, a wani samamen da aka kai a kauyen Barire.

Gwamntain ta Somaliya ta bayyana mutumin da Moalim Osman Abdi Badil. A wata sanarwar Ma'aikatar Yada labarai, gwamnati ta ce samamen da aka kai ranar 5 ga watan nan na Mayu, an yi shi ne karkashin jagorancin rundunar tsaron Somaliya ta kasa baki daya.

Gwamnatin ta Somaliya ta ce mutuwar ta Shugaban na al-Shabab Badil ta yi matukar kawo cikas ga harkokin kungiyar a yankin na Shabelle ta Kasa.

Bayanin na gwamnatin Somaliya bai yi bayyana ko Amurka ta taka rawa a wannan al'amarin na Barire ba, Ranar Jumma'ar da ta gabata, Amurka ta ce an kashe wani sojan kundunbalanta wajen wani samame, yayin da ya ke taimaka ma sojojin Somalaiya a yankin.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG