Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Sake Kama Wani Ba-Amurke


Koriya Ta Arewa ta ce ta sake damke wani ba-Amurke, wanda ta zarga da aikata laifi na yin karan tsaye.

Kafar yada labaran gwamnatin Koriya ta Arewa ta, KONA, ta ce an kama Kim Hak Song ranar Asabar. Rahoton ya ce ya taba aiki da Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Pyongyang, Jami'a mai zaman kanta daya tilo a duk fadin kasar ta Koriya Ta Arewa, wadda ta ke kuma da dinbin malamai daga kasashen waje fiye da yadda aka saba gani.

A wata takardar bayani, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce, "Kare lafiyar duk wani ba'Amurke na daya daga cikin abuwan da mu ka fi ba su muhimmanci. Muddun aka ce an kama wani ba-Amurke a Koriya Ta Arewa, to mu kan yi aiki ne da ofishin jakadancin Swedin da ke Pyongyang wajen kubutar da shi.

Kim Hak Song shi ne ba-Amurke na hudu da ke hannun Koriya Ta Arewa kuma kamun nasa ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da Koriya Ta Arewa ke dada hararan juna saboda shirin nukiliyar Koriya Ta Arewar. Tuni Shugaban Amurka Donald Trump ya tura wani jirgin ruwa mai dakon jiragen sama na yaki da bataliyansa daura da ruwayen na Koriya, a matsayin tauna tsakuwa game da manufofin wannan kasar mai bin tafarkin kwaminisanci.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG