Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Uganda 'yansanda sun sake cafke madugun adawa Kizza Besigye


Kizza Besigye madugun adawan kasar Uganda da 'yansanda suka sake cafkewa

Rahotanni daga kasar Uganda na cewa a yau Litinin ‘Yan sanda sun sake cafke dan takarar jam’iyyar adawa Kizza Besigye, kwanaki kadan bayan da ya fadi a zaben shugaban kasar da aka gudanar, wanda ya ce an tafka magudi a cikinsa.

Besigye ya shirya a yau Litini zai je hedkwatar hukumar zaben kasar domin tattara hujjojin cewa an tafka magudi, yayin da ya ke duba yuwuwar ko zai shigar da kara kan sakamakon zaben.

Jami’ain tsaro har ila yau sun kai wani samame a ofishin hedkwatar jam’iyyarsa, inda suka karbe kundin bayanan da ‘yan jam’iyyar suka tattara sakankon zabe.

Ko a makon da ya gabata, an tsare Besigye da wasu lokuta da dama, ciki har da ranakun da suka kai ga zaben da aka yi ranar Alhamis, wanda ya nuna cewa shugaba Yuweri Museveni ne ya lashe.

A ranar juma’ar da ta gabata, ‘yan sanda sun yiwa Besigye daurin talala, a wani mataki na hana shi jagorantar zanga zangar nuna adawa da nasarar da Museveni ya samu, wanda aka yi hasashen ka iya sa al’amura su rincabe. Shi dai shugaban ‘yan adawar ya yi kira ga magoya bayansa da su nuna rashin amincewarsu da tsare shi da aka yi, da kuma sakamon zaben.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG