Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Wasu Wurare An Kara Wa'adin Zabe Har Zuwa Jiya Lahadi


Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega

An gudanar da zabe lafiya amma kuma an samu wasu matsaloli da dama.

An kara wa’adin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisu a Najeriya har zuwa jiya Lahadi a wasu ‘bangarorin kasar, bayan da aka samu rahotannin wasu kura kurai a yankunan kasar, muamman a jihar River.

Mutane dai basu fito zaben ba kamar yadda aka fito lokacin zaben shugaban kasa,lokacinda shugaba Goodluck Jonathan ya zamanto shugaba na farko da aka ture shi daga kan mulki cikin lumana.

Jami’an hukumar zabe mai zaman kanta INEC a hedikwatar su dake Abuja, sunce an samu matsaloli har 66 a zaben da akayi na ranar Asabar, da aka fi ganin yawancin jihohin kudu da kudu maso gabashin Najeriya.

Masu nazarin zaben sunce akwai canji mai yawa a wannan zaben, masu takara a baya suna shirya magudi, ta hanyar satar akwatunan zabe, canza sakamakon zaben da shiga harkar bangar siyasa.

XS
SM
MD
LG