Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Jonathan Ya Cewa Buhari Ta Talho


Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, Maris 26, 2015.

Wani faifan sauti da ba a san wanda ya nada ba ya bayyana yadda shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kira Janar Muhammadu Buhari ya taya shi murnar lashe zabe.

Wata majiya daga fadar shugaban kasar Najeriya ta fitar da wani faifan sauti wanda ke nade da hirar shugaban Jonathan da Janar Muhammadu Buhari a lokacin da ya kira shi domin ya taya shi murna.

Wannan shi ne karon farko a tarihin siyasar kasar da aka doke shugaba mai ci a zabe har ma ya kira abokin hamayyarsa ya taya shi murna.

Ga dai yadda tattaunawar ta su ta kasance:

Buhari: Hello ranka ya dade,

Jonathan: Ranka ya dade, ya kake?

Buhari : Ina nan kalau ranka ya dade.

Jonathan : Ina mai taya ka murna

Buhari : Na gode kwarai ranka ya dade

Jonathan: To ya abaubuwa su ke?

Buhari: Ai ina ga ni ya kamata na yi maka barka, domin…..

Jonathan: Ya kamata ka samu wata rana ka zo saboda mu tsara yadda zan mika maka mulki.

Buhari: Haka, ranka ya dade, na gode kwarai.

Jonathan: To, ina mai taya ka murna.

Buhari: Ina mai girmama ka ranka ya dade. Na gode.

A ranar 29 na watan Mayu a ke sa ran za a rantsar da Buhari a matsayin sabon shugaban Najeriya, kasar da ta fi kowace yawan al’uma a nahiyar Afrika da tattalin arziki.

Yanzu haka Najeriyar na fama da matsalar tsaro da faduwar farashin mai da ma na naira a kasuwannin duniya. S

Sai dai wasu da dama na ganin batun kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a arewa maso gabashin kasar shi ne babban kalubale da sabuwar gwamnatin za ta fuskanta.

Baya ga haka akwai batun daliban Chibok da kungiyar ta sace su 200 yau kusan shekara guda wadanda har yau ba a jin duriyarsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG