Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Amsa Goron Gayyatar ‘Yan Majalisa Da Buhari Ya Yi


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

‘Yan Najeriya na ci gaba da yin tsokaci bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya amince zai bayyana a gaban Majalisar Dokokin kasar.

Shugaban ya amsa goron gayyatar a cewra Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila.

Gayyatar na zuwa ne kwanaki bayan kashe wasu manoman shinkafa da dama da mayakan Boko Haram suka yi a yankin Zabarmari da ke jihar Borno.

“Idan akwai abin da ya fi gabatar da sammaci ga shugaban kasa ya kamata ‘yan majalisa su yi. Saboda magana ta gaskiya it ace, ‘yan Najeriya musamman na arewaci mun gaji da uzurin da yake bayarwa,” a cewar wani mazaunin birnin Legas.

Lamarin ya janyo suka daga sassan duniya inda har Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da aka kashe ya kai 110.

A baya alkaluman da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutum 43 aka kashe.

“Kuma sai a ce mutane su ci gaba da hakuri, hakuri zuwa yaushe? Ya kara da cewa.

A ganin wasu ‘yan Najeriyar kuwa, gayyatar da aka aikawa shugaba Buhari an yi ta a makare.

“Wannan sammaci da ‘yan majalisa suka aikawa shugaban kasa ya yi kyau, amma ‘yan majalisar sun makara.” Wani mazaunin birnin na Legas daban ya fada.

A daya bangaren kuma wasu tuhuma suke yi kan kudaden tsaro da ake ba gwamnonin jihohi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya tura wata tawaga karkashin jagorancin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, don jajanta wa al'ummar jihar Borno kan kisan gillar da aka yi wa manoman shinkafar a kauyen Zabarmari.

Gwamnati ta kuma ce tana daukan matakan kawo karshen hare-haren mayakan na Boko Haram.

Wannan lamari dai ya ta da batun kiraye-kiraye da ake ta yi na cewa shugaban Najeriyar ya sauke manyan hafsoshin yayin da wasu ciki har da gwamnan jihar Borno ya ta da batun dauko dakarun haya domin dakile hare-haren ‘yan bindiga.

XS
SM
MD
LG