Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Zai Gana Da Majalisar Wakilan Najeriya Kan Matsalar Tsaro


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince ya gana da majalisar wakilai akan batun kalubalen tsaro da ake fuskanta a fadin kasar.

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana wa manema labarai hakan ranar Laraba 2 ga watan Disamba, bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Ya ce nan ba dadewa ba za a sanar da ranar da za a yi zaman ganawar.

A ranar Talata 1 ga watan Disamba ne majalisar wakilan ta yanke shawarar gayyato shugaba Buhari don ya yi wa ‘yan majalisar jawabi akan kokarin da ake yi na magance matsalolin tsaro a sassa dabam-daban na kasar, a lokacin da majalisar ta duba shawarar da wakilai daga jihar Borno suka gabatar biyo bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa wasu manoman shinkafa a kauyen Zabarmari da ke jihar a kwanan nan.

Ya kuma ce shugaba Buhari ya damu sosai da batun yanayin tsaro a kasar kuma zai yi wa ‘yan majalisar jawabin halin da ake ciki.

XS
SM
MD
LG