Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Yadda Za A Shawo Kan Matsalar Tsaro


Wasu 'yan banga da jihar Neja ke tallafawa don yaki da 'yan fashin daji
Wasu 'yan banga da jihar Neja ke tallafawa don yaki da 'yan fashin daji

Bisa ga yadda hare haren ta'addanci ke ci gaba da jefa rayukan ‘yan Najeriya cikin halin tsaka mai wuya, wasu daga cikin ‘yan kasar na ganin da gwamnatin tarayya za ta baiwa gwamnoni ikon bayar da umurni ga jami'an tsaro da watakila a iya samun saukin matsalolin.

Matsalar rashin tsaro a Najeriya musamman a yankin arewa tana ci gaba da hana jama'a barci cikin natsuwa ko kuma doguwar tafiya akan manyan hanyoyin kasar saboda rashin tabbas ga tsaron rayuka ko dukiyoyinsu sanadiyar ayyukan ‘yan bindiga.

Ko a ranar Larabar wannan mako, ‘yan bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyuka dake yankin sabon birni a gabashin cihar Sakkwato wadanda suka yi sanadiyyar salwantar rayuka da dukiyoyin jama'a.

Sa'idu Ibrahim Naino dan majalisar dokoki mai wakiltar yankin sabon birni a majalisar dokoki ta jihar Sakkwato ya ce ko kafin harin na wannan mako ‘yan bindiga sun kai farmaki a wasu garurwa.

Duk da cewa akwai jami'an soji da ‘yan sanda a yankin amma yanayin yadda suke karbar umurni kafin yin aiki yana mummunan tasiri ga shawo kan matsalar, sabanin yadda jama'ar yankin ke gani ga makwabtansu dake Jamhuriyar Nijar, a cewar wani mazaunin yankin na Sabon Birni Abdullahi Tsamaye.

Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da gurgunta al'amurra a Najeriya musamman a yankin arewa da ke fama da wasu matsaloli ko bayan matsalar tsaron.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Abin Da 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Yadda Za A Shawo Kan Matsalar Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00


XS
SM
MD
LG