Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abinda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Blinken Ya Fada Da Harshen Swahili a Kenya


Ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka a Kenya
Ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka a Kenya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya isa kasar Kenya, kasa ta farko da ya yada zango a ziyarar kasashen Afrika uku da zai kai wannan makon.

Babban jami'in diplomasiyan da ya ke ziyara a nahiyar Afrika karon farko tunda shugaban Amurka Joe Biden ya zabe shi ya rike wannan mukamin, ya bayyana kasar Kenya a matsayin kasar da Amurka ta dade tana abota ta kut-da-kut da ita.

Ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka a Kenya
Ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka a Kenya

Blinken ya wallafa a shafinshi na twitter jim kadan da saukar shi a tashar jirgin sama ta birnin Nairobi cewa,Vipi WaKenya! ma'ana, Yaya dai 'yan Kasar Kenya!


Ya kuma bayyana cewa yana marmarin ganawa da jami'an gwamnatin kasar Kenya da kungiyoyin farin kaya domin tattaunawa a kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma jadada muhimmancin dangantakar da ke tsakanin kasashen.

sakataren-harkokin-wajen-amurka-antony-blinken-zai-kai-ziyara-najeriya

blinken-ya-tattauna-da-takwaran-aikinsa-na-najeriya-onyeama

najeriya-na-so-amurka-ta-mayar-da-rundunar-sojin-africom-zuwa-afirka

Tuni al'ummar kasar da kuma masu kula da lamura kan harkokin nahiyar Afrika suka fara tsokaci dangane da ziyarar ta sa.

Yace "Mun gode da ka ziyarci kasashen Amurkawa bakaken fata. Ta haka ne kawai hukumomi za su iya ganin muhimman matsalolin da mu ke fuskanta zahiri a Afirka. Zai taimake ka ka yanke shawarar da ta dace ta shawo kan matsalolin da mu ke fuskanta kowacce rana."

Shi kuwa wannan cewa ya yi, "Na gode Ranka dade Sakatare domin lokacin da ka dauka domin ka ganewa idonka halin da ake ciki a Gabashin Afrika. Muna kira gare ka, ka tsaida shawarar da ta dace a madadin mutanen ka da kuma kasashen nahiyar Afrika."

Bayan kasar Kenya, Sakataren Harkokin wajen Amurkan Anthony Blinken zai kuma ziyarci kasashen Najeriya da kuma Senegal a ziyarar kwanaki biyar, daga 15-12 ga watan nan na Nuwamba da zai yi.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG