Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: 'Yan Bindiga Sun Kori 'Yan Sanda Daga Ofishinsu


Fulani masu garkuwa da mutane
Fulani masu garkuwa da mutane

Harin ya sa 'yan sandan dake aiki a wannnan ranar gudu daga ofishin lamarin da ya ba masu garkuwar damar awon gaba da wata mace da danta.

Bayan maharan sun kai hari ofishin 'yan sandan suka tasa keyar wadansu mutane biyu, sai dai bayan kama hanya maharan suka sake shawara suka saki biyu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da suka tafi da uwar da 'yarta.

A hirarta da Muryar Amurka daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su kafin aka sake su ta bayyana cewa, an yi garkuwa da su ne da karfe daya da rabi na rana ta kuma ce maharan sun kira suna neman kudin fansa.

Bayanai na nuni da cewa, wannan ne karo na uku da masu garkuwa suka shiga wannan gidan suna garkuwa da mutane da neman kudin fansa. Mai bayanin da ya nemi a saya sunansa bisa dalilan tsaro ya bayyana cewa, an yi garkuwa da mai gidan sau biyu yana dawowa kafin ya rasu, kana bayan makonni hudu da rasuwarsa, maharan suka dawo suka yi garkuwa da iyalinsa.

fulani-na-neman-kariya-daga-yan-sa-kai

sabuwar-dokar-hana-kiwo-a-jihar-lagoskungiyar-matasan-fulani-ta-soki-matakin-hana-kiwo-a-fili-a-kudancin-najeriya

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar Adamawa, DSP Suleiman Yahaya Guroji ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya kuma bayyana cewa maharan sun raba kansu ne wasu suka kai hari a ofishin 'yan sanda suka tarwatsa su, kana sauran suka shiga gidan marigayin suka yi garkuwa da uwargidansa da dansa.

Saurari rahoton da wakilinmu Salisu Muhammed Garba daga Adamawa:

Yan Bindiga Sun Kori 'Yan Sanda Daga Ofishinsu:3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG