Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Jimamin Mutuwar Dalibin Jihar Abia Da 'Yan Bindiga Suka Kashe


Makarantar Marist Comprehensive Academy
Makarantar Marist Comprehensive Academy

Al'umomin garin Okigwe da ke jihar Imo da na garin Uturu a jihar Abia, na ci gaba da jimami da alhinin mutuwar Donald Edeh, wani dalibin makarantar Marist Comprehensive Academy da ke garin Uturu, da 'yan bindiga suka harbe har lahira a yammacin ranar Asabar.

Mista Ogwulu Omalabo, wani dan kabilar Igala a jihar Kogi, shi ne direban motar da ta dauki marigayin da ma wasu daliban makarantar a lokacin da lamarin ya auku a iyakar Okigwe da Uturu, yayin da suke dawowa daga wani bikin nadin wasu limaman kungiyar Marist da aka gudanar a Orlun jihar Imo.

Ya ce, “Da muke dawowa, akwai motoci biyu a gabana. Akwai kuma mota guda tare da wata motar 'yan sanda a baya na. Sai muka wuce gidan gyara hali da ke Okigwe. Da zarar an wuce gidan gyara halin, akwai inda hanyar ta lankwashe zuwa garin Uturu, kuma wurin bai da kyau. Toh da muka danno wannan wurin, sai muka ga 'yan bindiga.”

Ya ci gaba da cewa “bayan da suka ganmu, sai suka bude wuta. A haka ne kowa ya fara tsalle daga mota, yayin da wasu suka arce cikin daji. Toh wannan buda wutar ne ya ritsa da wannan dalibinmu, kuma maharan sun yi garkuwa da wasu mutane a wata mota da ke gabanmu.”

Tuni an shiga zaman makoki a makarantar Marist Comprehensive Academy Uturu, inda wakilin Muryar Amurka ya tarar da malamai da dalibai da ma sauran ma'aikatan a cikin wani yanayin damuwa da kaduwa da alhini.

Rev. Joachim Ezetulugo shine shugaban makarantar, ya ce, “da misalin karfe biyar ne aka fara kira na ta waya da cewar akwai matsala. Da cewar dalibanmu da ke dawowa sun samu matsala a hanya. Ban san yanayin matsalar ba har sai wani ya kirawo ya ce an far wa dalibanmu.”

Mista Ezetulugo ya karkare da siffanta marigayi Donald Edeh a matsayin matashi mai saukin kai da biyayya, da kuma basira da hazaka.

Yanzu dai rundunar 'yan sandan jihar Imo ta ce ta na nan tana gudanar da bincike tare da karfafa tsaro akan wannan hanyar, kamar yadda kwamishinan 'yan sanda na jihar Malam Rabiu Hussaini ya shaidawa Muryar Amurka.

Domin karin bayani saurari rahotan Alphonsus Okoroigwe:


Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG