Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kafafen Yada Labaran Egypt Ba Sa Mana Adalci – Kocin Egypt


Lokacin da Mohamed Salah da sauran 'yan tawagar Egypt ke murnar doke Ivory Coast a gasar AFCON

A ranar Lahadi Egypt za ta kara da Morocco a zagayen quarter-finals a gasar ta AFCON.

Mai horar da ‘yan wasan kasar Egypt Carlos Quieroz ya yi korafin cewa kafafen yada labaran kasar ba sa yi wa ‘yan wasan kasar adalci.

A cewar Quieroz, kafafen yada labaran kasar ta Egypt suna yawan sukarsu tun da aka fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON a Kamaru.

A ranar Laraba ‘yan wasan na Pharoah suka cire Ivory Coast da bugun fenariti da ci 5-4 bayan da aka tashi a wasan babu wanda ya ci kwallo ko daya cikin mintina 120.

“’Yan wasan sun cancanci su kai zagaye na gaba, ina ga ya kamata a nuna musu girmamawa, tausayi da tare da nuna musu hakuri, musamman daga masu sharhi da kafafen yada labaran cikin gida, sun jima suna ta caccakar tawagar da ‘yan wasanta.” Quieroz ya ce.

Dan wasan Liverpool Mo Salah ne ya buga fenaritin karshe da ta ba Egypt nasarar shiga zagayen quarter-finals

Quieroz ya yi amfani da taron manema labarai da ake yi bayan kammala wasa, ya bayyana korafin nasa.

Egypt za ta kara da Morocco a zagayen na quarter-finals a ranar Lahadi.

A daya wasan da aka yi kuma, Equatorial-Guinea ita ma ta doke Mali da bugun fenariti.

Za ta hadu da Senegal a wasan quarter-finals a ranar Lahadi.

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG