Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFGHANISTAN: Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Sojoji Takwas


Jami'an tsaro a wajen Wani harin Kunar bakin wake da aka kai a Kabul

Wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa nakiya da aka dankare a wata mota kusa da sansanin sojoji dake kudancin Afghanistan ya kashe a kalla sojoji takwas ya kuma raunata wadansu da dama.

Yayinda yake tabbatar da adadin wadanda suka rasu a hirarsu da Muryar Amurka, Wani Kakaki a lardin yace an kai harin yau lahadi da safe ne a Nad Ali dake lardin Helmand inda ake fama da tashin hankali.

Nan da nan kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin. Wani kakakin kungiyar yace fashewar mai karfi ta “kashe ta kuma raunata” sama da jami’an tsaron Afghanistan 100, ko da yake kungiyar Taliban ta saba kara gishiri a adadin da take badawa.

Jami’an kasar Afghanistan sun fada yau lahadi cewa, an kai harin na yau ne a yankin da dakarun gwamnati suka kwace kwanan nan daga karkashin ikon mayaka.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG