Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kazamin Fada a Afghanistan Yayi Sanadiyar Mutuwar Jami'an Tsaro da Dama


Wani jami'in lardin Ghazni ya fada yau Talata cewa, 'yan kungiyar Taliban sun iya kwace gundumomi biyu, Jaghatu da Dehak, bayan wani mummunan fada a daren jiya.

Jami'an tsaron Afghanistan da dama sun mutu a kwanaki da yawa da suka kwashe suna gwabza kazamin fada da 'yan Taliban a wasu gundumomin lardin Ghazni a gabashin Afghanistan.

Wani jami'in gunduma, Latifa Akbar, ya ce 'yan sanda 20, ciki harda shugaban rundunar ‘yan sandan gundumar da kuma kwamandan 'yansanda na musamman na Dehak duk sun mutu a fadan da aka yi. Sai dai gwamnatin Afghanistan ta tabbatar da mutuwar mutane 12 kawai.

Mayakan Taliban sun kuma kashe wasu jami'an tsaro guda 20 a lokacin fadan a gunduma ta uku, Ajristan inda mayakan suka iya yiwa gidan shugaban gundumar kawanya shekaranjiya Lahadi.

Amma dakarun tsaro na musamman da aka girke don su taimakawa jami'an tsaron dake wurin sun fatattaki mayakan. Mai magana da yawun dakarun da suka yi fadan ya ce duk gine-ginen gwamnati na karkashin ikonsu. Ya kuma yi ikirarin cewa dakarun tsaron sun kashe ‘yan Taliban 10 a fadan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG