Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan: Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 19 Tare Da Jikata Wasu 50


Ana kwashe wadanda suka jikata

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a gabashin kasar Afghanistan lokacin da ake ci gaba da bukukuwan sallah ya rutsa da rayuka 19 tare da jikata wasu hamsin jiya Lahadi

A Afghanistan wani harin kunar bakin wake ya halaka, mutum sha-tara, kana ya jikkata wasu sama da hamsin a gabashin kasar.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan wani hari na daban da aka kai a yankin, wanda ya kaikaici dakarun gwamnati da mayakan Taliban da ke bikin murnar matsayar zaman lafiya da aka cimma, ta dan wani lokaci, domin a yi bukukuwan Sallah.

Harin shi ma ya auku ne a ranar Lahadi a Jalalabad, babban Lardin Nangarhar, inda ofisoshin gwamnati suke.

Dakarun kasar da mayakan Taliban na murnar ranar karshe ta bikin karamar Sallah ne,wacce ta biyo bayan azumin watan Ramadana da aka kammala.

Shi ma harin na Afgahnistan babu wanda ya dauki alhakin kai shi.

Jami’an Lafiya da masu ayyukan ceto sun ce akwai fargabar cewa adadin wadanda suka mutun zai karu.

Kwana guda, gabanin wannan hari, Kungiyar IS ta dauki alhakin wani harin kunar bakin wake da ya kashe mutum talatin-da-biyar a wajen birnin na Jalalabad.

Jami’an gwamnatin sun ce, daga cikin wadanda suka mutu akwai jami’an tsaron kasar ta Afghanistan, da mayakan Taliban da kuma fararen hula.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG