Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Tada Bam A Kabul


Tashin Bam

Wani dan kunar bakin wake ya tada bam a kusa da wani zauren babban taron malaman addinini wanda yawansu ya kai kimanin dubu biyu a Kabul baban birnin Afghanistan, abinda yai sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 7 da raunata da dama.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan yankin Hasmatullah Satnikzai ya shaidawa Muryar Amurka cewa harin ya auku ne a lokacin da daruruwan mutane ke barin wurin da akayi taron Loya Jirga, watau majalisar dattawan kasar, inda aka gabatarda wata sabuwar dokar adinin musulunci da ta haramta harin kunar bakin wake da kuma tashe tashen hankulan da ke faruwa a Afghanistan din.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki nauyin kai harin duk da cewa an san Mabiyan Kungiyoyin Taliban da na ISIS sun shahara wajen kai irin wadannan hare hare a Kabul.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG