Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ahmed Joda Ya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Hadin Kan Najeriya – Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

“Tun daga lokacin da aka kafa Najeriya har zuwa rasuwarsa, Joda ya ba da gagarumar gudunmowa wajen hadin kai da ci gaban kasar.”

Yayin da ake ci gaba da alhinin rasuwar tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya a Najeriya Malam Ahmed Joda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasar.

A ranar Juma’a Joda ya rasu a Yola da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya bayan wani tsawon lokaci da ya kwashe yana fama da jinya.

Buhari ya bayyana hakan ne a ta’azziyyar da ya aikawa iyalan mamacin da daukacin ‘yan Najeriya bisa wannan rashi.

“Tun daga lokacin da aka kafa Najeriya har zuwa rasuwarsa, Joda ya ba da gagarumar gudunmowa wajen hadin kai da ci gaban kasar,” wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Buhari Malam Garba Shehu ta ce.

“Ba za mu taba mantawa da sadaukarwarsa ba.” Buhari ya kara da cewa.

Shugaban kasar ya kuma ce, Joda, wanda “jarumin sakataren tarayya” ne na dindidin kamar yadda ake kiran wasu daga cikin wadanda suka yi aiki da shi cikin shekarun 1970’s, “ya yi fice a fannin ilimi, aikin jarida da na gwamnati da kuma harkar noma.”

A cewar Buhari, Joda, “gwarzo ne a idon kowanne dan Najeriya, wanda duk da cewa ya rasu, zai ci gaba da zama abin misali ga al’umomin da ke tafe a wajen nuna kauna, zaman lafiya da ‘yan uwantaka.”

Ahmed Joda, shi ne mutum na karshe da suka yi aiki da Gwamna Hassan Usman Katsina a zamanin mulkin gwamnatin arewacin Najeriya.

Shi ne kuma ya shugabanci kwamitin karbar mulki a 2015 da bayan da APC ta lashe zabe.

Ya rasu yana da shekara 91.

XS
SM
MD
LG