Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akufo-Addo Ya Bukaci a Gaggauta Sasanta Rikicin Mali


Taron kungiyar ECOWAS a Ghana
Taron kungiyar ECOWAS a Ghana

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo kuma shugaban kungiyar kasashen raya tattalin arziki ta Afrika ta yamma, ECOWAS, ya yi kira ga takwarorin sa shugabannin Afrika ta Yamma da su yi kokarin kawo karshen rikicin kasar Mali.

Akufo-Addo , ya ce bai yiwuwa kasar ta yi jinkiri wurin kafa gwamnatin damokaradiya bayan bore da sojpjin kasar suka yi a ranar 18 ga watan Agusta. Abin dake faruwa a Mali na bukatar gaggauta kawo shi karshe, inji shugaban na ECOWAS.

Nana Akufo-Addo ya yi wadannan kalaman ne a wurin wani taron wuni guda a Peduase Presidential Lodge a birnin Accra domin tattaunawa a kan batun kasar Mali.

Ya ce yana sa ran ganawar fuska da fuska tsakanin wakilai daga kungiyar ECOWAS da shugabannin sojin a Bamako zai iya samar da dama da zata kai ga samun mafita a wannan hali da ake ciki a kasar.

Ya ce ‘yan ta’adda suna amfani da wannan suna cin Karen su ba babbaka a Mali kana ya godewa madugun sojin kasar da amsa gayyata kuma ya halarci wannan taron na wuni guda.

Shugaban na ECOWAS ya tunasar da taron cewa ya kamata shugabannin sojin Mali su kafa gwamnati da zata yi aiki da tsari da kungiyar kasashen yankin ta gindaya musu a cikin watan Agusta.

Taron na Accra shine aikin farko da shugaba Akufo-Addo ya fara bayan da ya karbi ragamar shugabancin ECOWAS daga shugaban Jamhuriyar Nijer Mahamadou Issoufou, zai kuma ci gaba da aikin shiga tsakanin da kungiyar ta fara domin dawo da kasar Mali a kan tafarkin dimokaradiya.

Ga rahoton Ridwan Abbas daga Accra:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG