Accessibility links

Wani Jirgin Saman Yakin Sojan Najeriya ya Kashe Mutane Akalla 20 a Wani Kauyen Arewa Maso Gabas

  • Garba Suleiman

Kyaftin Ja’afaru Nuru na birged ta 23 ta sojojin Najeriya dake Yola, yace bay a da masaniyar wani hari ta sama da ya kasha fararen hula.

Mazauna wani kauyen da suka kubuta da rayukansu a kusa da bakin iyakar Najeriya da Kamaru, sun ce mutane akalla 20 aka kasha a kauyen nasu, a lokacin da wani jirgin saman yakin sojan Najeriya dake farautar maboyar ‘yan Boko Haram ya harba bam kan kauyensu.

Suka ce jirgin saman ya sako bam a kan kauyen Daglun, kuma akasarin mutanen da ya kasha tsoffi ne a saboda akasarin mutanen wannan kauye masu karfin jiki sun gudu a saboda hare-haren da ake kaiwa cikin ‘yan kwanakin nan a wannan yankin.

Kakakin sojoji, Kyaftin Ja’afaru Nuru na birged ta 23 ta sojojin Najeriya mai hedkwata a Yola, yace ba ya da masaniya game da wani hari ta sama da ya kashe fararen hula.

Wani dattijo a kauyen na Daglun ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa yana zaune a karkashin wata bishiya a lokacin da ya ga jirgin yana jefo bama-bamai. Wata ma’aikaciyar jinya a asibiti a yankin ta ce an kawo gawarwaki da kuma wadanda suka ji rauni da dama.

Wani shugaban al’ummar yankin yace mutane 20 suka mutu, wasu 25 kuma suka ji rauni.

Dukkansu sun nemi da a sakaye sunayensu a saboda fargabar fushin sojoji.

JIragen saman yakin soja, sun shafe makonni su na luguden wuta a yankin, a wani yunkuri na baya bayan nan na murkushe tsageran Boko Haram a wannan kasa da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka.

An kafa dokar ta baci watanni 9 da suka shige a wasu jihohi uku na arewa maso gabashin Najeriya.

A can baya ma, rundunar sojojin ta Najeriya ta fuskanci kura-kurai wajen kai farmaki daga sama.

A watan Janairun wannan shekara, wani jirgin saman yakin Najeriya ya jefa bama-bamai a kusa da kwambar motocin wani sanata wanda yake tafiya tare da rakiyar sojoji da ‘yan sanda. Babu wanda ya ji rauni. Rundunar sojan ta bayyana wannan lamari a zaman kuskuren aiki.

Har ila yau a cikin watan na Janairu, wani jirgin saman yakin sojan Najeriya ya kori ‘yan Boko Haram zuwa tsallaken iyaka a cikin Kamaru inda ya jefa bama-bamai uku a kan wata tashar kwastam ta Kamaru ya lalata motoci biyu.
XS
SM
MD
LG