Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al-Shabab Ta Kashe Akalla Mutane 15 A Somalia


Jami'an tsaron Somalia
Jami'an tsaron Somalia

Wasu fashewa guda biyu a gari Baidoa na Somalia sun kashe akalla mutane 15 kana wasu 30 kuma sun jikata.

Ministan watsa labarai a jihar kudu maso yammacin kasar, Ugas Hassan Abdi, yace wasu ‘yan kunar bakin wake su biyu ne suka kai wannan harin yayin da suke saye da damara dauke da abubuwar fashewa. Yace jami’ai na ci gaba da tantance mutane da fashewar ta taba su.

Kungiyar ta’addanci ta al-Shabab mai alaka da al-Qaida, wacce take rike da garin Baidoa tsakanin shekarun 2009 zuwa 2012 kafin dakarun gwamnatin Ethiopia ta koresu daga wurin, ta dauki alhakin kai wannan harin.

Wani da ya sha da kyar, ya fadawa sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, wani dan kunar bakin wake ne ya jefa gurneti a wani wurin cin abinci da jama’a suka taru, ya kashe akalla mutane mutane biyar kuma ya jikata wasu da dama.

Yace matashin ya tinkaro su kuma ya jefa musu gurneti a cikin wurin cin abinci mai cike da jama’a. Yace an dai harbe maharin kafin ya tada bam din jikinsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG