Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Mika Korafe-korafen Neman a Soke Zaben Kamaru


Hukumar zaben kasar Kamaru ELECAM, ta ce ta samu korafe-korafe har 25 na kiran a soke zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Lahdin da ta gabata.

Dantakara Cabral Libii, na jam’iyyar adawa ta Unvierse Party da Joshua Osih na jam’iyyar SDF, su biyun ne sukayi kira da a soke zaben.

Suna zargin an tafka magudi da kuma aringizon kuri’u domin baiwa jam’iyyar shugaban kasa Paul Biya, CPDM, damar lashe zaben.

Wani limani mai suna Rigobert Gabanmidanha na ‘Live and Peace Ministry’ shima yayi kira da a soke zaben. Yana ikirarin cewa hukumar dake tabbatar da sakamakon zaben tana karkashin shugaba Paul Biya ne, kuma dayawa daga cikin magoyan bayan jam’iyyun adawa ba a barsu sun kada kuri’unsu ba.

Ya ce yaje rumfar zabe da katin zabensa domin yin zabe, amma aka ce masa sunansa baya cikin jerin suyanen wadanda suka yi rijistar yin zabe.

Hukumar zaben Kamaru tana da wa’adin mako guda ta amsa korafe-korafen da aka gabatar mata. Haka kuma dole sai kotun tsarin mulki ta yanke hukunci kafin a bayyana sakamakon zaben ranar 22 ga wannan wata na Oktoba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG