Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'umman Kaduna Na Korafin Karuwar Aikin Yan Bindiga a Jihar


Fulani masu garkuwa da mutane
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:17 0:00

Fulani masu garkuwa da mutane

Al'umomin dake zaune a garuruwan da ke tsakanin Chukun, Udawa, Kuriga da Birnin Gwari sun ce hare-haren'yan-bindiga a yankin ya yi sanadin rashin garuruwan da ba su san adadin su ba.

A hirar shi da Muryar Amurka, daya daga cikin al'umar yankin, Malam Yusuf Ibrahim Udawa ya ce baya ga hare-haren yan-bindiga, su kan kuma shiga su karbi kudaden al'uma sannan su yi lalata da matan mutane.

Wannan korafi dai na zuwa ne kwanaki biyu da fitar da rahoton tsaro da gwamnatin jahar Kaduna ta yi inda ta bayyana nasarorin da ta ke samu kan maharan dajin baki daya.

Kaduna dai na cikin jihohin Arewan maso yammacin da ke fama da hare-haren 'yan-bindiga masamman dai satar dalibai wadda har yanzu akwai daliban makarantun da ba a dawo da su ba.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG