Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Jihar Kano Sun Koka Akan Sake Saka Dokar Kulle Da Gwamnatin Jihar Tayi


Al’ummar jihar Kano musamman kananan ‘yan kasuwa sun shiga rudani bayan mayar da dokar kulle da gwamnatin jihar ta yi sa’o’i kalilan bayan da gwamnatin tarayya ta dage dokar a jiya litinin.

Shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a Najeriya Boss Musatafa ya sanar da cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya amince da janye dokar kulle a dukkanin jihohin da gwamnatin ta sanya dokar a kwanakin baya.

Jihar Kano na daga cikin rukunin jihohin da gwamnatin tarayya ta kulle a baya bayanan, a wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Sai dai murna ta koma ciki ga al’ummar jihar Kano, musamman ‘yan kasuwa, domin sa’o’i kalilan bayan da gwamnatin tarayya ta bada sanarwar janye dokar kulle, gwamnatin jihar ta fito da wani jadawali dake nuna cewa, ranakun Laraba, Juma’a da kuma Lahadi kawai aka amince al’umma su fita domin hada-hadar yau da kullum.

Wannan mataki da gwamnatin jihar Kano bai yiwa kananan ‘yan kasuwa dadi ba, inda suke cewa,

Wakilin muryar Amurka yayi kokari domin jin ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar Kano Mohd Garba, domin fayyace wannan mataki na gwamnati tare dayin tsokaci akan wancan zargi na wasu ‘yan kasuwa, amma bukata ta bata biya ba.

A hannu guda kuma wasu daga cikin cibiyoyin lafiya a jihar sun fara farfado da ayyukan su duk kuwa da wannan sarkakiya ta dokar kulle a Kano.

Kakakin Asibitin koyarwa na Aminu Kano Hajiya Hauwa Abdullahi tace, suna daukar matakan kariya a asibiti, suna tabattar da cewa kowa ya saka takunkumin rufe fuska ko kuma matakin bada tazara.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00


Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG