Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Koriya Ta Arewa Na Bukatar Sake Ganawa Da Shugaban Amurka


Kim DaTrump

Shugaban Koriya Ta Kudu, da kansa ya isar da wani sako ga Shugaban Amurka Donald Trump, cewa, Shugaban Koriya Ta Arewa na son ya sake ganawa da shi nan ba da jumawa ba don cigaba da shirin kawar da nukiliya a yankin ruwan Koriya.

"Labudda, kai ne kadai za ka iya warware wannan matsalar," abin da Shugaban Koriya Ta Kudu, Moon Jae-in, wanda ya gana da Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un a makon jiya, ya gaya ma shugaba Trump kenan.

Sai shi kuma Shugaban na Amurka ya amsa da cewa, "Ina iya ganawa ta biyu da Shugaba Kim kwanan nan." To saidai ba a tsai da wurin ganawar ba, to amma ta yiwu ba a Singapore bane, inda ya gana da Shugaban na Koriya Ta Arewa a karon farko ranr 12 ga watan Yuni.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG