Accessibility links

Alhazan Najeriya Sun Mika Koke Da Korafe-Korafe

  • Halima Djimrao

Alhazan Najeriya sun koka cewa an ajiye su da nisa a Mina, a tazarar tafiyar kilomita 4 da kafa zuwa wurin jifan shedan

Amirul Hajj, Mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn el-Kanemi, alhazan na Najeriya suka mikawa korafe-korafen

Shugaban tawagar gwamnatin tarayyar Najeriya a aikin Hajjin bana, mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn el-Kanemi ya ce ya samu korafe-korafe da dama daga alhazan Najeriya a lokacin da ya ziyarci masaukan su a Makka. A taron manema labaran da mai martaba Shehun Bornon ya kira a birnin Jeddah, ya fada cewa korafe-korafen suna da matukar mahimmanci kuma za su sanya su a cikin rahoton da za su mikawa gwamnatin Najeriya idan sun koma gida. Wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari na cikin manema labaran da Shehun Borno ya yiwa bayani a birnin Jeddah:

XS
SM
MD
LG