Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkalin Alkalan Najeriya Tanko Mohammed Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa


Babban alkalin Alkalan Najeriya, Muhammad Tanko.
Babban alkalin Alkalan Najeriya, Muhammad Tanko.

Alkalin Alkalan ya sanar da hakan ne a wata wasika da ya aikewa shugaban Najeriya ranar Litinin.

WASHINGTON, DC - Babban alkalin Najeriya Tanko Muhammed ya sanar da yin murabus daga mukaminsa bisa dalilan rashin lafiya a wata wasika da ya tura wa Shugaba Muhammadu Buhari, a cewar kafafen yada labaran kasar.

Hadimin Mohammed na musamman a fannin yada labarai, Isah Ahuraka ne ya tabbatar wa manema labarai batun.

Muhammed dan shekara 68 da haihuwa, ya kasance babban alkali a kotun kolin kasar tsawon shekara 3, ko da yake tun a shekarar 2005 ya ke aiki a kotun kolin kasar.

A watan Janairun shekarar 2019 ne shugaba Buhari ya rantsar da Mohammed a matsayin mukaddashin alkalin alkalan kasar, bayan dakatar da tsohon babban alkali Walter Onnoghen.

Ana sa ran rantsar da alkali na biyu mafi girma a kotun kolin, Olukayode Ariwoola daga jihar Oyo a matsayin mukaddashin alkalin alkalan, a cewar jaridar Premium Times ta Najeriya.

Murabus din Muhammad na zuwa ne mako guda bayan da alkalai 14 daga cikin 16 a Kotun Kolin kasar, ciki har da Ariwoola, suka koka kan shugabancin Muhammad, inda suka ce ya gaza magance bukatu da matsalolin abokan aikinsa, a cewar wata takarda da aka fallasa. Hakan kuma na zuwa ne kusan watanni 18 kafin lokacin da ya kamata Mohammed ya yi murabus a hukumace, wato a watan Disamban shekarar 2023, lokacin da zai cika shekaru 70 da haihuwa.

XS
SM
MD
LG