Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkawarin Atiku Na Hadin Kai Da Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya


Abubakar Atiku
Abubakar Atiku

A ranar Asabar ne dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce zai samar da zaman lafiya da hadin kai a kasar tare da inganta tattalin arzikinta yayin da ya ke yakin neman zabensa na karshe.

WASHINGTON, D.C - Matsalolin tattalin arziki da suka hada da hauhawar farashi mafi girma a kusan shekaru ashirin da suka gabata, rashin aikin yi da karancin kudade, da kuma rashin tsaro da aka dade ana fama da shi, da tashin hankalin 'yan aware na daga cikin abubuwan da ke damun masu kada kuri'a a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Atiku Abubakar a wajen gangamin siyasa
Atiku Abubakar a wajen gangamin siyasa

Atiku mai shekaru 76 a duniya daga babbar Jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party, ya na daga cikin manyan ‘yan takara uku da ke neman matsayin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda zai sauka daga mulki bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi a mako mai zuwa.

Duk da kiraye-kirayen da Atiku ya yi na kasa, akalla kuri’un jin ra’ayin jama’a guda hudu sun nuna cewa yana bin ‘dan takarar Jam’iyyar ‘yan tawaye Peter Obi daga karamar Jam’iyyar Labour da kuma Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki.

Hedkwatar Jam'iyyar PDP
Hedkwatar Jam'iyyar PDP

A karkashin taken yakin neman zabe na “Alkawarina ga ‘yan Najeriya”, Atiku ya yi alkawarin kara shigar da kamfanoni masu zaman kansu cikin harkokin tattalin arziki domin samar da ayyukan yi da bunkasa ababen more rayuwa. Yana son mayar da kamfanin Mai na kasa NNPC Ltd zuwa wani kamfani, ya samar da dala biliyan 10 ga kananan ‘yan kasuwa da fara tattaunawa da masu fafutukar ballewa don kawo karshen tashe-tashen hankula a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Atiku ya shaidawa dimbin magoya bayansa a wani filin wasa da ke Jiharsa ta Adamawa, a Arewa maso gabashin kasar, inda ya ce "Mun yi alkawarin yin jagoranci bisa alkawuran da muka dauka domin tabbatar da cewa mun samu kasa daya dunkulewar kasa, kuma mun samu zaman lafiya da kuma tattalin arziki."

Wannan dai shi ne karo na uku da Atiku ya yi yunkurin jagorantar kasar da ta fi kowacce yawan Jama'a a nahiyar Afirka, kuma masu sharhi na ganin hakan na iya zama na karshe ga tsohon mataimakin shugaban kasar wanda zai kai shekaru 80 a zabe mai zuwa nan da shekaru hudu.

-Reuters

XS
SM
MD
LG