Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Tayi Barna A Jihar Adamawa


Hotun ambaliyar ruwa a Jihar Bauci, wadanda aka dauka Alhamis 15 ga Agusta.

Rahotanni na cewa kawo yanzu fiye da kauyuka 116 ne ambaliyar ruwa ta mamaye a kananan hukumomi 12 cikin 21 na jihar Adamawa, biyo bayan sako ruwa daga madatsar ruwan Lagdo dake kasar Kamaru.

Ambaliyar dai ta janyo an samu asarar muhalli da gonaki da dabbobi, baya kuma ga asarar rayuka lamarin da yanzu ma ya jefa mutane cikin mawuyacin hali. Wasu mutanen da wannan al’amari ya shafa sun bayyana irin halin da suka shiga dama asarar da ta janyo musu.

Sai dai kuma shugabannin al’umomin da abin ya shafa sun zargi gwamnatin Najeriya ne da rashin kulawa da batun na madatsar ruwa ta Lagdo, da kowacce shekara kan jawo asara ga ‘yan Najeriya.

Kwamishinan yada labaran jihar Adamawa Kwamarad Ahmad Sajo, yace akwai kwamiti da gwamnatin jiha ta kafa wadda hakkin ta ne ta bincika da tabbatar da ainishin wadanda wannan ambaliya ta ritsa da su, taga irin illa da asarar data janyo don ganin irin taimakon da za’a basu, amma akwai taimakon gaggawa da suka hada da irin su tabarmi da katifu da kayan abinci da aka riga aka kai musu.

Masana dai na gargadin za’a iya samun bullar annoba a mafakar wadanda ambaliyar ta shafa.

Saurari Rahotan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG