Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Faransa Sun Ja Kunnen Laurent Gbagbo


Sojoji masu yin biyayya ga Laurent Gbagbo su na kokarin tarwatsa magoya bayan Alassane Ouattara a wata unguwa mai suna Abobo dake birnin Abidjan, alhamis 16 Disamba 2010

Kasashen biyu sun ce idan bai sauka nan da 'yan kwanaki kadan ba, za su dauki matakan garkama masa takunkumi da iyalansa da kuma mukarrabansa

Amurka ta ja kunnen Laurent Gbagbo cewa idan bai sauka daga kan karagar mulki nan da 'yan kwanaki kadan ba, to zai dandana kudarsa.

Haka shi ma shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya ce tilas ne Mr. Gbagbo ya sauka ya mika mulki cikin wannan makon, ko kuma Kungiyar Tarayyar Turai za ta kafa masa takunkumi.

Mr. Sarkozy da kuma Amurka sun yi wannan gargadi nasu a yau jumma'a, a yayin da kasar Ivory Coast take fuskantar yiwuwar karin mummunar zanga-zanga da fitina a tsakanin sassa biyu masu gaba da juna a wannan dambarwar siyasa.

Mr. Gbagbo ya ki yarda ya sauka ya mika mulki ga Alassane Ouattara, mutumin da duniya ta amince da cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi cikin watan da ya shige a kasar Ivory Coast.

Mr. Ouattara yayi kira ga magoya bayansa da su yi maci yau Jumma'a a Abidjna, birni mafi girma a kasar, domin su sake yin kokarin kwato gidan telebijin na kasar dake hannun magoya bayan Mr. Gbagbo.

A kokarin da ya ci tura na neman kwato ginin a jiya alhamis, an kashe mutane akalla 20 a ba-ta-kashin da aka yi a tsakanin magoya bayan Mr. Ouattara da sojoji masu yin biyayya ga Gbagbo.

Ya zuwa tsakar rana a yau jumma'a, babu wani rahoton da aka samu na karin zanga-zanga ko arangama.

A yau jumma'ar kuma, Firayim ministan kasar Kenya, Raila Odinga, ya ce tilas ne Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta cire Mr. Gbagbo karfi da yaji daga kan mulki domin tabbatar da kare dimokuradiyya.

Hukumar 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fada a yau Jumma'a cewa 'yan kasar Ivory Coast su fiye da dubu 4 da dari biyu sun gudu zuwa kasar Liberiya a saboda fargabar cewa wannan rikicin siyasa zai kai ga zub da jini.

XS
SM
MD
LG